fidelitybank

Masu zanga-zangar tsagaita wuta Gaza sun katse sakataren harkokin wajen Amurka lokacin jawabi

Date:

Masu zanga-zanga da ke kiran a tsagaita wuta a Gaza, sun katse Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken a lokacin wani zaman sauraron jin bahasi na Majalisar Dattijai ranar Talata.

Mutane da yawa sun yi cincirindo suna ta kuwwar “A tsagaita wuta yanzu!”

Sakatare Blinken da Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin na gabatar da jawabi ne game da bukatar fadar White House ta neman amincewa da kudin tsaro dala biliyan 106.

Kudin ya kunshi dala biliyan 14.3 don tallafawa kokarin sojojin Isra’ila a kan kungiyar Hamas. In ji BBC.

Suna tsaye daya bayan daya, masu zanga-zangar sun jira har lokacin da Mista Blinken ya fara bayar da bahasi kafin su fara yi masa ihu. Anthony Blinken dai ya dakata yayin da ‘yan majalisar ala tilas suka jingine zaman a lokuta da dama.

‘Yan sandan da ke kula da ginin majalisar dokokin sun yi hanzari suka rako masu zanga-zangar daga zauren a lokacin da suka fara ihu.

‘Yan sanda sun ce an kama mutum 12 saboda yin zanga-zanga ba bisa ka’ida ba a cikin wani sashe na majalisar.

Wasu daga cikin wadanda suka katse zaman majalisar na da alaka da wata kungiya mai adawa da yaki wadda ake kira CODEPINK, ta kuma yi kira ga Amurka ta daina tura makamai Ukraine.

Masu zanga-zangar da dama sun daura kyalle mai rubutu “Ba mu yarda da yi wa Gaza kofar rago ba”, daidai lokacin da suke kira ga Amurka ta dakatar da tura wa Isra’ila kudade.

Kungiyar CODEPINK ta tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin wakilanta.

Ta ce wasu sun sanya jan fenti a hannuwansu “don nuna alamar jini”. Mista Blinken ya yi nuni da masu zanga-zangar a karshen sanarwarsa da cewa, ga kuma “jijiyoyin wuyan da aka tayar a wannan daki”.

“Dukkanmu mun dukufa wajen kare fararen hula. Dukkanmu mun san irin wahalhalun da ake ciki a daidai wannan lokaci da muke magana, dukkanmu mun dukufa wajen ganin karshen haka,” a cewarsa.

Sai dai ya kara da cewa, abu ne mai muhimmanci ga Amurka ta mara baya ga abokan kawancenta.

taraba news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp