fidelitybank

Masu zanga-zanga sun rushe gidan tsohuwar Firaministar Bangladesh

Date:

Masu zanga-zanga a Bangladesh, sun ci gaba da afka wa gine-gine masu alaƙa da iyalan tsohuwar firaiministar ƙasar Sheikh Hasina wadda aka hamɓarar da gwamnatinta a shekarar da ta gabata tare da cinna wuta.

Daruruwan mutane yawancinsu dalibai ne suka yi amfani da ƙananan motocin ruguza gine-gine wajen farfarasa abubuwa da farwa gidan mahaifin tsohuwar firaiministar, Sheikh Mujibur Rahman, wanda shi ne shugaban ƙasar na farko, bayan samun ‘yancin kan ƙasar daga Pakistan.

Haka kuma masu zanga-zangar sun lalata gidajen biyu daga cikin ƙusoshin jam’iyyar tsohuwar firaministar, tare da cire allunan da ke ɗauke da sunanta ko na danginsu daga jami’ar ƙasar da ke birnin Rajshahi.

Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan da aka samu labarin Sheikh Hasina za ta yi wa magoya bayanta jawabi ta shafin sada zumunta daga Indiya, inda ta gudu bayan hamɓarar da ita a watan Agustan bara.

vanguardnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp