Gwamnatin jihar Kano ta ce, bata-garin da suka afka wa babbar kotun jihar yayin zanga-zanag kan tsadar rayuwa sun kwashe takardun tuhumar da ake yi wa tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje kan cin hanci da rashawa.
Ganduje ne shugaban jam’iyyar APC na ƙasa mai mulkin Najeriya a yanzu bayan ya mulki Kano tsawon shekara takwas a ƙrƙashin jam’iyyar.
“Abin takaici ne a ce wasu maƙiyan Kano sun ɗauko hayar wasu domin lalata gine-gine masu tarihi da zimmar kare tsohon Gwamna Ganduje da iyalansa daga shari’ar cin hanci,” a cewar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf lokacin da ya kai ziyara kotun a ranar Laraba.
Gwamnatin Kano ƙarƙashin jam’iyyar NNPP na tuhumar Ganduje, da matarsa Hafsat, da ɗansa Umar, da wasu mutum biyu bisa zargin karkatar da biliyoyin kuɗaɗe a lokacin mulkinsa.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature, ya fitar ta ƙara da cewa masu zanga-zanagr sun lalata “kusan kowane ɓangare na kotun da jawo asarar sama da naira biliyan ɗaya” ta hanyar sace kayayyaki, da ƙona motoci.