Masu zanga-zanga daga jihar Zamfara a ranar Juma’a sun mamaye kofar shiga hedikwatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
Suna rokon hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta sake bude bincike kan tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle.
A cewar gidan talabijin na Channels, masu zanga-zangar a karkashin inuwar jam’iyyar APC Loyalists Forum na son hukumar EFCC ta binciki duk wasu korafe-korafen da ake yi wa tsohon gwamnan.
Hakan ya hada da karkatar da kwangilar da ake zargin ta kai har naira biliyan 70 a lokacin yana gwamnan jihar.
An ce Daraktan Hulda da Jama’a na EFCC, Wilson Uwujaren ne ya karbi takardar zanga-zangar a madadin shugaban.
Ya kuma tabbatar wa masu zanga-zangar cewa EFCC ta kuduri aniyar bin duk wata shari’a ta cin hanci da rashawa domin cimma matsaya mai ma’ana.