Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Juma’a, ta gargadi masu zanga-zangar da su ka hana jama’a zaman lafiya a hanyar Legas zuwa Abeokuta su shiga taitayin su.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ya yi wannan gargadin a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, a Ota, Ogun.
Oyeyemi ya ce jama’a na da ‘yancin yin zanga-zanga, amma bai kamata su kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ba.
“‘Yan sanda ba za su bar mutane su haifar da tashin hankali ta hanyar karya doka a jihar,” in ji shi.
Kakakin ya ce an tura dukkan kwamandojin ‘yan sandan yankin ne domin wanzar da zaman lafiya a hanyar Legas zuwa Abeokuta.
NAN ta ruwaito cewa wasu fusatattun masu zanga-zangar sun tare manyan hanyoyin Sango-Ota, Ifo, Papa da Itori da ke kan hanyar Legas zuwa Abeokuta, saboda kin karbar tsoffin takardun kudi na N500 da N1,000.
Wakilin NAN da ya bi diddigin lamarin ya lura cewa an ga masu zanga-zangar suna wasan kwallon kafa a titin mota yayin da masu ababen hawa da fasinjoji suka makale na tsawon sa’o’i.
Wani direban dan kasuwa, Mista Tope Bankole, ya ce galibin gidajen mai ne suka haddasa zanga-zangar, saboda sun ki karbar tsohuwar kudi N500 da N1,000.
Bankole ya ce yana da sama da Naira 130,000 na kudin N1,000, inda ya ce ya yi kokarin yin amfani da wasu kudaden wajen siyan man fetur amma aka ki amincewa da tsohon kudin.
A cewarsa, gidajen mai ya kamata su rika karbar wadannan tsofaffin kudade domin direbobin ‘yan kasuwa suna kashe kudaden ne a gidajen mai.
“Ba za a sami matsala ba idan gidajen mai suna karbar tsofaffin takardun kudi na N500 da N1,000,” in ji Bankole.
Ya ce tabarbarewar kudi da rashin iya fitar da kudi daga na’urar ATM da kuma rashin karbuwar tsofaffin takardun kudi ta gidajen mai na shafar talakawa.
Bankole ya ce talakawa suna yakar kansu alhali masu hannu da shuni ba sa jin zafi.
Daya daga cikin masu zanga-zangar Ismail Sanni, ya ce sun yanke shawarar bayyana kokensu ne saboda rashin karban tsofaffin takardun kudi na N500 da N1,000.
Sanni ya ce matsalar kudi da ake fama da ita a halin yanzu, rashin cire kudi daga na’urar ATM da kin amincewa da tsofaffin takardun kudi ya jawo wa talakawa zafi.
Ya ce gazawar talakawa wajen fitar da kudadensu daga bankunan na kawo cikas ga rayuwar talakawan Najeriya.
NAN ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya ce ya kamata a yi amfani da tsohuwar N200 tare da sabbin takardun har zuwa ranar 10 ga Afrilu, yayin da tsofaffin takardun N500 da N1,000 suka daina zama dillalan doka a kasar.