fidelitybank

Masu zanga-zanga na yunkurin juyin mulki a Burkina Faso

Date:

Masu zanga-zanga a Burkina Faso sun ƙona shelkwatar jam’iyya mai mulki a Burkina Faso ta MPP a Ouagadougou babban birnin ƙasar.

Rahotanni na nuni da cewa ‘yan sanda sun samu nasarar tarwatsa su da hayaƙi mai sa hawaye bayan sun far wa ginin.

Masu zanga-zangar sun ƙona tayoy, inda suke goyon bayan sojojin da ke yunƙurin juyin mulki da kuma neman manyan jami’an ƙasar da su sauka daga kan mulki.

Haka kuma masu zanga-zangar na neman a ƙara ƙaimi a yaƙin da ake yi da masu iƙirarin jihadi waɗanda ke ƙara zafafa hare-hare a ƙasar.

Masu zanga-zangar dai sun fito ne sa’o’i bayan da aka yi musayar wuta mai ƙarfi a wasu sansanonin sojoji a Ouagadougou da garuruwan da ke Arewacin ƙasar.

Gwamnatin ƙasar ta yi kira da a zauna lafiya, kuma ta musanta yunƙurin da ake yi na juyin mulki a ƙasar.

today nation

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp