fidelitybank

Masu zanga-zanga ku guji haddasa rikici a Kwara – NSCDC

Date:

Kwana uku kenan da shirin gudanar da zanga-zangar a fadin kasar nan, kwamandan hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Kwara, Umar Mohammed, ya gargadi masu zanga-zangar da da su gujewa aikata miyagun laifuka tare da haddasa tarzoma a jihar.

Ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Ayoola Michael Shola ya fitar a Ilorin.

Umar ya bayyana cewa rundunar tana cikin shirin ko ta kwana, tare da daukar kwararan matakai na tabbatar da bin doka da oda kafin muzaharar, da lokacin da kuma bayan zanga-zangar.

Ya kuma kara da cewa rundunar ba za ta nade hannayenta tana kallon ‘yan iska suna barna, da barnata muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa ba, domin za a samar da isassun kayan aiki a fadin jihar domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Yayin da yake amincewa da ‘yancin ‘yan kasa na gudanar da zanga-zangar, kwamandan Umar, ya bukaci matasa da sauran ‘yan kasa da su bayyana kokensu bisa doka da lumana, tare da tabbatar da cewa tsaron kasa da lafiyar jama’a ba su taka kara ya karya ba.

Ya kuma ja kunnen Kwaran masu bin doka da oda da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsoro ba, yana mai tabbatar da cewa an dauki tsauraran matakai don tunkarar barazanar da ake shirin yi.

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp