Gamayyar ƙungiyoyin daga arewacin Najeriya sun jaddada cewa ba gudu ba ja da baya za su fito zanga-zangar da suka ce za su jagoranta a sassan arewacin kasar, duk da gargaɗi da roƙon gwamnati su ƙara haƙuri su jingine zanga-zangar.
Ƙungiyoyin sun shirya gudanar da zanga-zangar ta kwana 10 daga ranar Alhamis 1 ga Agusta.
Sun ce zanga-zanga ita ce kawai zaɓin da ya rage masu domin nuna fushinsu kan halin da Najeriya ke ciki na matsalolin tattalin arziki da tsaro.
Amma hukumomin gwamnati na ci gaba da gargaɗin yiyuwar tashin hankali kuma wasu na iya amfani da zanga-zangar su wawushe dukiyoyin al’umma.
Farashin kayan masarufi a Najeriya sun yitashin gauron zabi da ba a taɓa gani ba a tarihi, ɗaya daga cikin dalilin da ke ingiza zanga-zangar da ta ja hankali a shafukan sada zumunta.
Masu shirin jagorantar zanga-zangar kuma yanzu sun fito sun faɗi dalilansu da kuma buƙatu da yadda suka tsara gudanar da zanga-zangar.


