Aƙalla masu zanga-zangar nuna adawa da ƙarin haraji a Kenya 8 ne aka tabbatar da mutuwarsu a birnin Nairobi bayan da suka mamaye harabar majalisar jim kadan bayan da ‘yan majalisar suka amince da sabon tsarin ƙrin haraji, a cewar wani rahoto da gidan talabijin ta KTN TV mai zaman kanta ta fitar.
Gidan talabijin ɗin ya ruwaito cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon hargitsin da ya biyo baya yayin da ‘yan sanda suka yi yunkurin hana masu zanga-zangar shiga harabar majalisar.
Hotunan bidiyo da aka yi ta watsawa a shafukan sada zumunta sun nuna gawarwakin mutane da kuma mutanen da suka jikkata yayin zanga-zangar.
Rahotanni sun ce ‘yan sandan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin daƙile masu zanga-zangar da suka mamaye majalisar.
An kuma ƙona wani ɓangare na ginin majalisar.
Kafofin yada labaran cikin gida sun kuma bayar da rahoton cewa an kwashe ƴan majalisar cikin gaggawa zuwa wasu gine-ginen da ke kusa.
Matasan Kenya ne dai suka jagoranci zanga-zangar neman a janye kudirin kasafin kudin shekarar 2024, wanda ya gabatar da sabbin ƙarin ƙudin haraji.