Darakta Janar na hukumar yi wa kasa hidima (NYSC), Shuaibu Ibrahim, ya gargadi masu yi wa kasa hidima kan yin tafiye-tafiye da daddare.
Ya yi wannan gargadin ne a wajen bikin karrama ɗaliban kashi na Batch A Stream 2, na shekarar 2022 a jihar Sokoto.
Shuaibu wanda ya samu wakilcin kodinetan NYSC na jihar Sokoto, Muhammad Nakamba, ya ce, ana sa ran ‘yan masu yi wa ƙasa hidima su rika rage tafiye-tafiyen da suke yi da karfe 6:00 na yamma, domin rage hadurran da ke faruwa a kan tituna.
Shugaban masu yi wa kasa hidima na NYSC ya ba da shawarar cewa, idan tafiyar ta kama a dare, to su yi kokarin kwana a barikin sojoji ko kuma duk wani wurin da aka kebe na zaman lafiya.
Ya kuma gargade su game da munanan dabi’un zamantakewa kamar shaye-shayen miyagun kwayoyi, safarar miyagun kwayoyi, aikata laifuka ta yanar gizo da kuma zamba.