Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya), ya bukaci matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) su yi gwajin kwaya yayin da suke gabatar da aikin yi wa kasa hidima na shekara daya a sansanonin wayar da kan jama’a daban-daban a fadin kasar nan.
Ya ce wannan wani bangare ne na kokarin rage bukatar muggan kwayoyi da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ke yi.
Marwa ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin Darakta-Janar na NYSC, Brig. Janar Mohammed Fadah, wanda ya jagoranci tawagar gudanarwar sa a wata ziyarar ban girma da suka kai hedikwatar NDLEA a ranar Laraba a Abuja.
Shugaban hukumar ta NDLEA ya ce, matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya tare da hujjoji da alkaluma daga binciken da aka gudanar a shekara ta 2018 kan magungunan na kasa yayin da ya yi kira da a yi kokarin hada kai don sauya labarin.