Zababben Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya yi gargaɗi cewa duk wasu masu gine-gine a filayen tsibirin jihar da su dakata nan take.
Wannan sanarwa na kunshe ne cikin wani sako da zababben gwamnan ya wallafa Juma’a a shafinsa na Facebook.
A cewarsa, “kamar yadda muka kudiri aniyar dawo da tsarin birnin Kano, ina shawartar jama’a da su daina duk wani aikin gine-gine a filayen gona, a ciki da wajen tsare.
Karanta Wannan: Duk lokacin da na ga Abba ya dauka a kan layi zan a ƙarar da shi – Kwankwaso
“Wuraren addini da na al’adu, da dukkan asibitoci, da makarbarta, da kume gefen katangar birnin Jihar Kano [ganuwa].”
Haka kuma, a kunshin da mai magana da yawun zababben gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, an kuma sanar da rushewa ko kuma ci gaba da aikin duk wasu gine-gine a filayen jihar.