Gwamnatin jihar Katsina ta ce masu tsegunta wa ƴanbindiga bayanai ne ke haddasa kashi 80 cikin 100 na hare-haren yanbindiga a faɗin jihar.
Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Nasir Mua’azu ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a jihar.
Nasir Mu’azu ya ce masu kwarmata wa ƴanbindigar bayanai da ke kai musu abinci da sauran abubuwa ne ke ba su bayanan da suke buƙata domin ƙaddamar da hare-hare.
Kwamishinan ya ce hakan kuma na matuƙar kawo wa gwamnati tsaiko wajen yaƙi da matsalar ƴan fashin daji a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin irin waɗannan mutane kan kai wa ƴanbindigar abubuwan da suke buƙata har dazuka su kuma sayar musu a farashi mai tsada.
“A ɗaya daga cikin waɗannan garuruwa an taɓa kama wani mutum na sayar da kwalbar lemo naira 3,000 ga ƴan bindiga, wani kuma na sayar musu man fetur kan naira 5,000 kowace lita”, kamar yadda ya bayyana.
“Haka ma akwai masu kai miyagun ƙwayoyi su sayar musu a farashi mai yawa, sun mayar da hakan sana’ar da suke samun kuɗi masu yawa”, in ji shi.
Kwamishinan ya yi zargin cewa wasu ma daga ciki kan haɗa baki da ƴanbindigar wajen sace mutanen da suke so a sace ciki kuwa har da danginsu.