fidelitybank

Masu tsafi sun cire sassan jikin wani Yaro a Adamawa

Date:

Wasu da ake kyautata zaton masu tsafi ne sun kashe wani yaro a Yola babban birnin jihar Adamawa tare da cire wasu sassan jikinsa.

An tsinci gawar yaron ne a unguwar Rumde da ke bayan sakatariyar karamar hukumar Yola ta Arewa a Jimeta, inda aka yanka masa makogwaro tare da cire masa harshe da ido.

An bayyana wanda aka kashe a matsayin dalibin daya daga cikin makarantun islamiyya da ke yankin.

Wasu mazauna garin na Rumde sun bayyana jin kukan yaron, sai dai sun ce ba su dauki mataki ba, domin a tunaninsu kawai cin zarafin wani karamin yaro ne da wani babba ya yi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Yahaya Nguroje, ya ce an kai gawar yaron asibiti domin a duba gawarwakin yaron, kuma tuni aka fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata laifin.

Ya bukaci iyaye da masu kula da su da su rika daukar nauyin tarbiyyar ‘ya’yansu a koda yaushe.

Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa marigayin wanda dan makarantar Tsangaya Islamiyya ne, da alama yana daya daga cikin wadanda aka shigo da su garin Yola daga wani gari mai nisa domin karantar addinin Islama da Larabci.

vanguard news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp