Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana fara shirin rancen dalibai, sabon mafi karancin albashi na N70,000 da kuma kafa tsarin bashi na masu amfani a matsayin dalilan da bai kamata ‘yan Najeriya su fara zanga-zangar wahala da ake shirin yi a ranakun 1-10 ga watan Agustan 2024 ba.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar shugabannin addinin Musulunci karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau, a fadar gwamnati ranar Alhamis.
Tinubu ya bukaci masu shirya zanga-zangar da kada su mayar da Najeriya Sudan.
A cewarsa, gwamnatinsa na sake yin wani shiri na jin dadin jama’a domin kaiwa kowane dan Najeriya mara karfi a matakin farko.
“Muna sake aiwatar da tsarin jin dadin jama’a don isa ga matakin unguwanni, wanda shine mafi kusanci ga mutanenmu. Za mu tabbatar da cewa mun sake kulla alaka da unguwanni, domin mu ba da alawus-alawus ga talakawa da marasa galihu.
“Lamunin dalibai zai biya kudin makaranta. Za a sami tallafin kuɗi don ilimin yaranmu. Lamunin mabukaci zai tallafa wa ’yan ƙasa don siyan motoci da gidaje, kuma za su iya biya a hankali.
“Mun kara mafi karancin albashi da fiye da kashi 100,” in ji shi.
A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da sabuwar dokar mafi karancin albashi bayan Tinubu da ma’aikatan Najeriya sun amince da N70,000 mafi karancin albashi.
Tun a makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta fara bayar da kudade ga mutane 110,000 da suka ci gajiyar shirin rancen dalibai na Naira biliyan 35.
Wannan na zuwa ne watanni bayan da gwamnatin Tinubu a watan Afrilu ta amince da karbo bashin Naira biliyan 100 ga ‘yan Najeriya.