Shugaban Uganda, Yoweri Museveni, ya gargadi masu shirya zanga-zangar yaƙi da cin hanci da rashawa da aka shirya yi a ranar Talata cewa, ahir dinsu, domin kuwa a cewar sa “suna wasa da wuta”.
Ya ce zanga-zangar ba za ta kasance bisa ka’ida ba, kuma masu zanga-zangar suna “aiki da wasu kasashen wajen don haifar da hargitsi a Uganda.
Zanga-zangar kin jinin karin haraji a Kenya ce ta zaburar da matasan Ugandan.
Tun da farko a ranar Asabar, ‘yan sandan Uganda sun shaida wa masu shirya zanga-zangar cewa ba za su amince da ita ba.
Sai dai masu shirya ta sunce babu gudu ba ja da baya.
Sun kuma yi fatan za su wuce majalisar dokokin kasar, wadda suke zargin da taimaka wa gwamnati wajen aiwatar da cin hanci da rashawa. In ji BBC.