Kungiyar Masu Sana’ar Buredi ta MBA reshen Jihar Zamfara, ta umarci mambobinta da su daina yin biredi har sai sun sasanta da gwamnatin jihar kan dokar hana daukar biredi a babura.
Kungiyar ta karyata ikirarin cewa mahaya babur dauke da biredi suna ba da biredi ga ‘yan fashi a dazuzzukan.
A kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta haramtawa duk wani babur da ke dauke da biredi, inda ta ce suna kai wa ‘yan fashi da ke aiki a jihar biredin.
Gwamnatin ta kuma haramta sayar da man fetur a gwangwani, inda ta nunar da cewa biredi da gwangwanin man na karfafa gwiwar ‘yan ta’addan wajen kai hare-haren ta’addanci a kan mazauna yankin.
Da yake zantawa da manema labarai a Gusau, Sakataren Kudi na kungiyar na Jihar, Malam Habibu ya bayyana cewa kungiyar ba za ta koma yin biredi ba har sai ta sasanta da gwamnatin jihar.
“Mun jima muna gudanar da tarurruka da gwamnatin jihar domin warware matsalar. Ina da yakinin cewa nan ba da dadewa ba za a warware matsalar,” ya kara da cewa.