Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) Peter Obi, ya ce masu rangwamin hankali ne suka mamaye siyasa da mulki a Najeriya.
Obi ya yi wannan jawabi ne a wani taro da aka yi a taron Men of Valor mai taken ‘Navigating the Corridors of Power: The Church and Politics,’ wanda Revival House of Glory, Abuja ya kira.
Obi ya jaddada cewa, dole ne ‘yan Najeriya su dauki mataki a yanzu domin tabbatar da shugabanci nagari.
A cewarsa, mahaukaci a gwamnati ne kawai zai saci naira biliyan 80 daga baitul malin gwamnati.
Ya kuma yi gargadin cewa kasar nan za ta ci gaba da shan wahala matukar gurbatattun ‘yan siyasa ba su ba da dama ga mutanen da suka cancanta ba.
Obi ya ce, “Ba za mu iya barin wannan ’yan daba ta ci gaba ba, ya kamata ‘yan Nijeriya su kwato kasarsu. Kashi 70 cikin 100 na wadanda ke siyasa a yau bai kamata su sami dalilin zama a wurin ba. Na fadi haka, siyasa a Najeriya al’amari ne da mahaukata suka karbe mafaka.
“Wannan ita ce kawai kasar da mafi muni ke jagoranta. Ni dan kasuwa ne kuma a hankali na shiga siyasa. Lokacin da kuka ɗauki fiye da yadda kuke buƙata kuna rashin lafiya.