Babban Bankin Kasa (CBN), ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan Yuli cewa, masu sana’ar POS su kammala yin rajista da Hukumar (CAC).
An bayyana hakan ne lokacin da aka yi wata ganawa tsakanin kamfanonin hada-hadar kuɗi na ƙasar nan da shugaban hukumar ta rajistar kamfanoni, Hussaini Magaji a Abuja ranar Talata.
Da yake jawabi a wurin taron, shugaban na CAC ya ce, wa’adin watanni biyu na yin rajistar ya yi daidai da ka’idojin doka da kuma umarnin babban bankin Kasa CBN.
Wata sanarwa da CAC ya fitar kuma ta kara da cewa, an ɗauki matakin ne domin kare masu mu’amala da kamfanonin hada-hadar kuɗi tare kuma ƙarfafa tattalin arziƙin kasar nan.