Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, ya ce ya kamata masu neman kujerar Majalisar Tarayya su mutunta shawarar Jamâiyyar APC da zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu.
Wike yace mutunta shawarar APC da Tinubu zai kawo cigaban Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake bayyana cewa babu wani Shugaban kasa da zai iya gudanar da aiki a iyakar karfinsa idan ba shi da hadin kan Majalisar Dokoki ta kasa.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Wike ya ce: âA lokacin yakin neman zabensa, shi, Tinubu, ya yi alkawarin hada kan kowane dan Najeriya tare da kawo kwarewa.
“Ba zai zama ba saboda ku ‘yan APC ne ko a’a, muna son ‘yan Najeriya masu karfin taimakawa mutane wajen isar da abin da zai sa Najeriya ta zama babba.
âBabu wani shugaban kasa da zai iya yin kyau sosai idan ba shi da wannan shugabancin da ba ya shirye ya ba shi hadin kai. Idan kun tuna abin da ya faru a cikin 2015, wannan ya shafi aikin gwamnatin yanzu.
“Don amfanin ‘yan Najeriya, su mutunta shugabancin jam’iyyarsu da kuma zababben shugaban kasa don ci gaba.”