Masu shigar da kara da ke neman a tsawaita wa’adin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun yi watsi da shari’ar duk kuwa da yanke hukunci a gaban karar zaben shugaban kasa.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a hukuncin da kotun ta yanke mai lamba: FHC/ABJ/CS/656/23 da Justice Initiative for the disadvantage and the appressed Persons da Lawman Nzenwa, na 1 da na 2 suka shigar da kara kan lamarin.
Mai shari’a Ekwo, wanda ya lura cewa wadanda suka shigar da karar ba su kasance a gaban kotu ba a ranar da aka dage zaman na karshe, ya ce ya bayar da umarnin a mika masu kara da sanarwar sauraren shari’ar na yau.
Alkalin ya ce ya kuma bayar da umarnin a kira masu karar ta wayar tarho tare da aike musu da sakon tes domin sanar da su yadda lamarin ke gudana.
Sai dai ya bayyana mamakinsa cewa wadanda suka shigar da karar ko lauyansu ba sa cikin kotu.
Mai shari’a Ekwo ya ce na yi imanin wadanda suka shigar da kara da kuma lauyoyinsu sun fahimci cewa abin da suke nema bai dace ba kuma ba za a taba iya ba.
“Da alama masu shigar da kara da lauyansu sun gudu; sun yi watsi da lamarinsu,” in ji shi.
Don haka alkalin kotun ya ce tun da wadanda suka shigar da karar ba sa kotu kuma ba zai iya bayar da oda ba a lokacin da ba su nan ba, don haka ya yi watsi da karar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ta ruwaito cewa masu shigar da kara ta hannun lauyansu, a ranar 12 ga watan Mayu, sun shigar da karar mai dauke da kwanan wata 12 ga watan Mayu.