Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Jigawa bisa mutuwar mutane kusan 140 sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a ranar Talata.
Al’ummar Majia da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa sun jefa cikin rudani a ranar Talatar da ta gabata sakamakon fashewar tankar da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.
Ko da yake rundunar ‘yan sandan Jigawa ta bayyana a ranar Laraba cewa mutane 90 ne suka mutu a lamarin, shaidun gani da ido sun ce sama da mutane 140 ne aka binne a ranar Laraba bayan aukuwar lamarin.
Da yake mayar da martani, IGP a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Alhamis ya bukaci masu ababen hawa da su rika bin ka’idojin tsaro a kullum.
Ya kuma yabawa kokarin jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an agajin gaggawa kan matakin da suka dauka na kashe gobarar, da kwashe wadanda abin ya shafa, da kuma tabbatar da an dawo da zaman lafiya cikin gaggawa a yankin.
IGP, yayin da yake addu’a ga rayukan wadanda suka rasu, ya tabbatar wa da jama’a “tsare-tsare na wayar da kan jama’a game da illolin da ake samu na diban mai da sauran ayyukan makamantansu”.