fidelitybank

Masu mota ku kauracewa titin Lokoja zuwa Abuja – Gwamnati

Date:

Ma’aikatar kula da ayyuka da gidaje ta kasa, ta bukaci masu motoci da ke tafiya zuwa arewacin kasar daga yankin kudu ko gabashin kasar da su kaurace wa titin Lokoja zuwa Abuja.

Babban jami’in da ke kula da ayyuka na ma’aikatar a jihar Kogi Injiniya Jimoh Kajogbola, shi ne ya bayar da shawarar a wata sanarwa inda ya yi kira ga matafiyan da su yi amfani da wasu hanyoyin.

Kiran ya biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye wasu sassan titin ne a yankin Koton-Karfe bayan da Kogin Kwara ya tumbatsa.

A sanarwar jami’in ya shawarci masu motocin da za su je Abuja daga kudu maso yamma su bi ta titin da ya tashi daga Ilori ya bi ta Mokwa ya wuce ta Bida.

Su kuwa matafiya daga yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu an shawarce su da su bi ta titin Makurdi zuwa Lafia.

Sanarwar ta bukaci masu motocin da suma suke daga arewacin kasar da su bi wadannan hanyoyin da aka bayar da shawarar masu fitowa daga yankin kudun zuwa arewa su bi, har zuwa lokacin da ruwan ya ja baya.

Jami’in ya shawarce su da su bi titin lAbuja zuwa Lafia ya wuce ta makrdi zuwa Otukpa ko kuma wanda titin Abuja zuwa Bida ya bi ta Mokwa ya wuce ta Jebba.

Wannan matsala ta ambaliya a titin na Lokoja zuwa Abuja ta haddasa matsalar karancin mai a yankin babban birnin tarayya Abuja, kasancewar motocin dakon mai ba sa iya wucewa.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp