Hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, ta gargadi masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar da su guji amfani da tayoyin hannu da aka fi sani da tokunbo.
Kwamandan sashin na jihar Jigawa, Ahmed Muhammad ya yi wannan gargadin a ranar Juma’a a wajen kaddamar da yakin neman zaben 2022 da aka gudanar a filin ajiye motoci na Inshora, Dutse.
Ya ce taken yakin neman zaben na bana shi ne “A guji wuce gona da iri, da yin lodi, da tayoyin da ba su da aminci su isa da rai”
Ahmad ya bayyana cewa kashi saba’in na yawan hadurran kan tituna na faruwa ne sakamakon wuce gona da iri kuma ya bukaci direbobi su guji yin amfani da tayoyin Tukumbo wajen gujewa hadurran tituna.
A nasa jawabin kwamandan shiyyar, ACM Godwin Omiko ya ce wannan gangamin na wayar da kan jama’a ne kan illolin da ke tattare da karya dokokin hanya.