Wani sabon bincike ya nuna cewa ba a taba samun yawan masu kudi irin yanzu ba a duniya.
Binciken na shekara-shekara da kamfanin bayar da shawarwari na duniya Capgemini, ya yi ya ce mutanen da suka mallaki kadarorin zunzurutun kudade na miliyoyin daloli sun ƙaru da sama da kashi biyar cikin ɗari a bara zuwa kusan miliyan 23.
Jimillar dukiyarsu ta kai kusan tiriliyan 87, wanda hakan ya ninka yawan arziƙin da ake samu a cikin Amurka (GDP) sau uku.
Bincike ya nuna an samu wannan cigaba ne sakamakon bunƙasar kasuwannin hannun jari a dalilin samuwar fasar AI.
Brazil da Faransa sun bukaci haraji mafi kankanta kan attajiran duniya domin rage tazarar da ke tsakanin masu kudi da talakawa.