fidelitybank

Masu kiwon Kaji sun koka yadda wasu basa iya siyan Ƙwan Kaza a Najeriya

Date:

Kungiyar masu kiwon kaji a Najeriya ta koka kan yadda ‘yan Najeriya da dama ba za su iya siyan kwai ba saboda tabarbarewar tattalin arziki.

Hussaini Gumel, kungiyar PFAN reshen jihar Jigawa ne ya bayyana haka a lokacin da suka kai wa gwamna Umar Namadi ziyarar ban girma a ranar Alhamis a gidan gwamnati dake Dutse babban birnin jihar.

A cewar Gumel, “Tun da aka cire tallafin man fetur, masana’antarmu ta shiga tsaka mai wuya, ‘yan Najeriya da dama ba sa iya sayen kwai, kuma tallace-tallacen mu ya yi kasa a gwiwa.”

Ya danganta raguwar tallace-tallacen da karuwar matsalolin tattalin arziki da ‘yan Najeriya da dama ke fuskanta.

“Muna kokawa don ci gaba da kasuwancinmu.

“Babu kasuwar kayayyakinmu, kuma rashin isassun kudade da ke yawo a tsakanin mutane abu ne mai ban tsoro,” in ji Mista Gumel, yana mai gargadin cewa kasuwancin na gab da durkushewa.

Rahotanni na cewa, yanzu haka ana siyar da kwandon kwai a kasuwannin Najeriya tsakanin Naira 5,700 zuwa 6,000, ya danganta da wurin da ake ciki.

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Har yanzu ina LP kuma ni ne zan iya saita Najeriya – Datti

Datti Baba-Ahmed, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a...

APC ta zama buhun kusa ta gaza a Najeriya – Amaechi

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Chibuike Amaechi ya bayyana jam'iyyar...

An fara samun takun saka tsakanin Turkiyya da Najeriya a kan kungiyar Gulen

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta bukaci shugaban kasar...

Arziƙin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 a farkon 2025 – NBS

Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 cikin...

Kamfanonin lantarki za su katse wutar lantarki saboda bashi

Kamfanonin samar da wutar lantarki, sun ce suna iya...

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...
X whatsapp