Hukumar gidan gyara hali ta Najeriya ta ce ana samun ƙaruwar yawan fursunonin da ke jiran a zartar masu da hukuncin kisa a sassa daban-daban na ƙasar.
Kakakin hukumar na jihar Kano, SCS Musbahau Lawan Ƙofar Nasarawa ne bayyana haka a hirarsa da BBC.
Ya ce a yanzu haka da yawa daga cinkinsu sun kwashe shekara goma zuwa ashirin ba a aiwatar masu da hukuncin ba, abin da aka ƙiyasta ƙaruwar da 98 cikin 100.