fidelitybank

Masu jamhuru ne suka kitsa magana ta tsakanin Kiristoci da Musulmai – Shettima

Date:

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya nesanta kansa da wasu kalamai da ya ce “ba daidai ba ne, kuma masu hatsari” da wasu ke alaƙantawa da shi.

Wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran mataimakin shugaban ƙasar ya fitar, ta ruwaito Kashim Shettima na cewa, kalaman da ake ambatawa ya furta lokacin wani taro da sanatoci ranar Lahadi wasu masu jamhuru ne suka kitsa a yunƙurinsu na nuna rashin dacewar ‘yan takara Musulmai da ke neman shugabancin Majalisar dattijai.

Sanarwar ta zo ne bayan wani bidiyo da ke ta yawo a shafukan sada zumunta wanda a ciki aka jiyo Kashim Shettima lokacin gabatar da jawabi, yana cewa “A wajena idan ana maganar wannan gwamnati, Kirista mafi lalacewa kuma mafi rashin ƙwarewa daga Kudancin Najeriya, ya fi Musulmin Arewa na-ƙwarai a kan muƙamin shugaban majalisar dattijan tarayyar Najeriya”.

Ya ce ba a bayyana kalaman a muhallin da aka yi su ba, kuma an canza musu ma’ana don kawai su dace da manufar masu zagon ƙasa ga burin al’ummar Najeriya na tabbatar da haɗin kan ƙasa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a yayin taron da ‘yan majalisar dattijai masu gangamin ganin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin sun jagoranci majalisar dattijai ta goma, Kashim Shettima ya jaddada tsarin siyasar ƙasar inda ya yi nuni da cewa samun Kirista daga kudancin Najeriya da kuma wani Musulmi daga Arewaci shi ne zai tabbatar da daidaiton adalci don inganta muradin shigar da kowa a dama da shi a gwamnatin tarayya.

Ta ce kalaman Sanata Kashim Shettima sun taso ne sanadin wani gagarumin gangami game da rarrabuwar da ke tsakanin al’ummar ƙasar, kuma sun dace da alƙawarin jam’iyya mai mulki na ganin an dama da kowa a dukkan lardunan da rukunonin al’umma.

Ta ambato Sanata Shettima yana nunar da cewa, bisa la’akari da ganin shugaban Najeriya da mataimakinsa duk Musulmai ne, to ba zai kasance rashin kan gado ga ‘yan majalisar ba, idan suka zaɓi ɗan takarar da ba Musulmi ba, ko da kuwa akwai Musulmin da ya fi cancanta, saboda tabbatar da daidaito.

A cewarsa, abin fargaba ne idan aka jirkita irin wannan roƙo maras harshen damo don nunar da cewa mataimakin shugaban ya ce duk lalacewar Kirista ya fi ɗan takara Musulmi.

Kashim Shettima ya ce rashin kan gado ne ma a ce mataimakin shugaban ƙasar wanda shi kansa Musulmi ne, zai iya ƙasƙantar da ƙwarewar ɗan’uwansa Musulmi a ƙasar da Musulmi ke jagoranta, har ma ya nuna nagartar shugabancin da babu kamarta, bisa doron da aka zaɓe su ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC a watan Fabrairun da ya wuce.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp