Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC), a ranar Talata, ta gargadi masu yi wa kasa hidima da aka tura jihar Gombe, da su guji hawa motar baki a matsayin rage musu hanya.
Babban Darakta Janar na NYSC, Birgediya-Janar Mohammed Fadah ne ya ba da wannan shawarar a sansanin horar da ‘yan gudun hijira na wucin gadi da ke Amada a karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe, a yayin bikin rufe kwas din ‘B’ Stream I Orientation Course na shekarar 2022.
Fadah ya ce, yana da kyau ‘yan kungiyar su kasance masu lura da tsaro a ko da yaushe kuma su guji ayyukan da ka iya jefa rayuwarsu cikin hadari.