Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi watsi da sabuwar haɗakar ƴan hammayar ƙasar, waɗanda ya bayyana da masu haushin rashin gwamnati a hannunsu.
Yayin da yake jawabi a gidan talbijin na Channels ta cikin shirin Sunrise Daily, Gwamnan ya ce shirin haɗakar ADC ba wani abu ne face tsantsar yaudara.
“Ya kamata mu faɗa wa kanmu gaskiya, lokacin yaudarar mutanen Najeriya fa ya ƙare”, in ji shi.
A makon da ya gabata ne gamayyar wasu ƴan hamayya daga jam’iyyu daban-daban suka haɗe kai ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC da nufin ƙalubalantar gwamnatin APC a 2027.
Ƴan hamayyar sun zargi gwamnatin APC da lalata Najeriya da kuma yunƙurin mayar da ƙasar mai bin tafarkin jam’iyya guda.
To sai dai Gwamnan na Katsina ya ƙalubalanci masu haɗakar da cewa me suka yi wa Najeriya a lokacin da suke riƙe da madafun iko.
“Wane ne a cikinsu ba ya cikin gwamnatin da ta gabata? Waye a cikinsu bai taɓa shiga gwamnati ba? Muna sane da irin abubuwan da kowanensu ya yi,” in ji Gwamnan na Katsina.
“Mun san irin abubuwan da suka yi lokacin da suke gwamnati, sai yanzu za su zo suna ɓaɓatu saboda ba sa cikin gwamnati.” a cewar Gwamna Radda.