Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da wasu ma’aurata, Sunday Odoma Ojarume da matarsa, Janet Odoma Ojarume a kauyen Sheda da ke yankin karamar hukumar Kwali a Abuja.
Wani mazaunin Sheda, Japhet Musa, ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, inda ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane dauke da manyan makamai ne suka mamaye al’umma.
Ya ce, masu garkuwa da mutanen sun ajiye kansu ne a wurare masu mahimmanci a cikin al’umma, kafin sauran ’yan bindigar su zage damtse shingen wadanda abin ya shafa suka tafi da su da bindiga.
“Hakika kauyen Sheda ya kasance cikin tashin hankali ranar Lahadi, saboda harbe-harbe da masu garkuwa da mutane suka yi a kai-a kai a cikin al’umma, kafin su je su yi garkuwa da mutumin da matarsa,” in ji shi.
Ya kara da cewa, ko da yake daga baya masu garkuwa da mutane sun sako matar tare da neman ta ta je neman kudin fansa ga mijinta.
Aminiya ta tattaro cewa, harbe-harben bindiga da aka yi a lokacin farmakin ya haifar da tashin hankali a tsakanin
daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FCG) Kwali, wadanda ke dakunan kwanan su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, har yanzu bai mayar da martani ga sakon da aka aike mata ba domin jin ta bakinsa game da sabon harin da aka yi na garkuwa da mutane.
Tuni dai aka rufe FGC Kwali saboda iyaye sun kwashe ‘ya’yansu.