fidelitybank

Masu garkuwa sun hallaka wani dan kasuwa a Ondo

Date:

A karshen makon da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da Augustine Okoye, wani dan kasuwa a Ugbe da ke karamar hukumar Akoko ta Arewa maso Gabas a jihar Ondo.

Marigayin, shahararren mai sayar da kayan shafawa a yankin Ikare-Akoko na jihar an ce an kashe shi ne bayan an biya kudin fansa da ba a bayyana ba.

An dai sace Okoye da matarsa ne a kan babbar hanyar Isua-Ise Akoko a kan hanyarsu ta zuwa garin Isua.

Masu garkuwa da mutanen sun sako matar tare da kashe dan kasuwan bayan sun karbi kudin fansa daga danginsu.

Da take bayyana yadda aka sace su, matar, Bolaji Augustine, ta bayyana cewa an kashe Okoye kafin a biya kudin fansa.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, wata majiyar ‘yan sanda a Ikare Akoko ta ce an gano motar da aka yi amfani da ita wajen sace mutanen daga wurin da lamarin ya faru.

Majiyar ‘yan sandan ta kara da cewa jami’an hukumar Amotekun da ’yan banga a yankin sun fara tseratar dajin domin kwato gawar Okoye tare da cafke wadanda ake zargin.

bbc news nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An ceto Mutane 25 da syka kife a kwale-kwalen Sokoto

Hukumomi a jihar Sokoto sun ce, sun samu nasarar...

An fara duba rabon gyaran arzikin Najeriya

Shugaban Hukumar rarraba arziƙin ƙasa RMAFC, Mohammed Shehu, ya...

Kwallaye 6 da aka zurawa Santos a raga ta sanya Neymar ya fashe da kuka

Ɗan wasan tawagar Brazil, Neymar ya fice daga cikin...

Hukumar Shari’a ta magantu kan sadakin dubu 20 da ya yamutsa hazo a Kano

Hukumar shari’a ta jihar Kano, ta ce ba a...

Cutar Mashako ta yi ajalin Yara hudu a Kano

Rahotanni na cewa cutar mashaƙo wadda aka fi sani...

Cin zaben da NNPP ta yi a Kano cuwa-cuwa ne – Ata

Ministan Jiha na Gidaje da Cigaban Birane, Rt Hon...

Mutane kusan 40 sun ɓace sakamakon haɗarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale...

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...
X whatsapp