Masu garkuwa da tsohon sakataren hukumar kwallon kafa ta ƙasa (NFF), Sani Toro da tsohon mataimakin Kociyan Super Eagles, Garba Yila da daya daga cikin abokansu Isa Jah, na neman a sako su akan Naira miliyan 150.
Rahotanni sun bayyana cewa, Toro da wasu sun bar daurin auren dan gidan tsohon shugaban NFF, Aminu Maigari a Abuja ranar Asabar, da misalin karfe 05:00 na yamma a kan hanyarsu ta zuwa Bauchi, inda aka yi garkuwa da su da misalin karfe 07:00 na dare a jihar Nasarawa.
Wata majiya ta iyali ta ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci N150m a matsayin kudin fansa.
“Eh, gaskiya ne shi (Isa Toro) yana tuki tare da abokansa guda biyu lokacin da aka yi garkuwa da su jiya (Asabar). Masu garkuwa da mutane suna neman kudin fansa naira miliyan 50 ga kowannen su”, majiyar ta kara da cewa masu garkuwan sun zanta da mai gidan nasu, Maigari.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin.
Wakili, ya ce: “Labarin gaskiya ne. Na ci karo da daya daga cikin ‘ya’yansa, wanda ya shaida min cewa, an yi garkuwa da shi ne a hanyar Akwanga a Nasarawa a lokacin da yake dawowa daga Abuja.”