fidelitybank

Masu garkuwa da mutane su na amfani da Macizai wajen kashe mutane – Wanda suka shaƙi iskar ƴanci

Date:

Mutanen da suka shaƙi iskar ‘yanci daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su sun bayyana cewa mutanen da suka sace sun a amfani da macizai masu dafi domin tsorata su.

Wasu a cikinsu da suka bayyana halin da suka tsinci kansu a ciki a hirar da suka yi lokuta daban-daban da kamfanin dillancin labarai na NAN, sun ce akwai macizai masu tarin yawa a cikin dajin da ‘yan bindigar suka mamaye.

Sun ce macizan suna yawan sarar masu garkuwar da mutanen da aka sace.

Ɗaya daga cikin mutanen da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa NAN cewa masu garkuwar sun jefa su cikin matattarar macizai.

“Masu garkuwar sun san wuraren da macizai suke kuma suna ajiye mutanen da suka sace a nan.

“Da zarar sun ga macizai, masu jin tsoronsu sai su yi ta neman guduwa. Ganin macizan na tsoratar da su.

“Lokacin ne waɗanda aka sace suke neman ‘yan uwa da abokan arziki su sayar da komai – gida da fili da motoci da kayan gida da takalma, komai ma – kawai don a haɗa kuɗin fansa.”

Binciken da NAN ya yi ya gano dazukan da ke da mafi yawan macizai suna Birnin Gwari a jihar Kaduna da Kala-Balge kusa da tafkin Chadi a jihar Borno.

Wasu yankunan sun haɗa da Shaki a jihar Oyo da Borgu da Kagara a jihar Neja sai Karim Lamido a Adamawa da Lau a jihar Taraba.

Wasu cikin mutanen da suka kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar sun shaida wa NAN cewa lamarin ya ƙazanta a yanzu ganin yanayin zafin da ake ciki yayin da macizan ke barin ramukansu da nufin neman abinci da shan iska

latest news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp