Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, a ranar Juma’a, ya ce, kuskure ne a bangaren masu laifi da masu fashi da makami su dauka suna yakin addini.
Shehu Sani, wanda ya rubuta a shafin sa na Facebook da aka tabbatar, ya ce, ba za a taba daukar su a matsayin yaki mai tsarki ba.
Sanata Shehu Sani ya rubuta cewa: “Sun yi ikirarin yakin addini ne. Sun kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
“Suna yin garkuwa da su har da mata da yara na tsawon watanni ko shekaru. Wani lokaci su kan yi fyade tare da cin zarafin wadanda abin ya shafa.”
A cewarsa, suna jawo wa iyalai wahala da kunci tare da karbar kudin fansa.
“Wannan ba kuma ba zai taba zama yakin addini ba. Kuma ba za su taɓa zama mayaka masu tsarki ko wanne iri ba. Suna rayuwa ne kawai da takobi… ”in ji shi


