Shugaban makarantar Apostolic Faith Group inda aka sace dalibai biyar da malamai hudu a jihar Ekiti, ya ce masu garkuwa sun yi barazanar ɗaukan mataki kan mutanen da suka sace idan aka gaza biyan kudin fansar da suka nema.
Gabriel Adesanya ya shaida wa BBC cewa akwai kimanin dalibai 20 da ke cikin motar lokacin da masu garkuwar suka kai musu hari.
Ya ƙara da cewa, “da yawa daga cikin iyayen yaran ba su da ko kashi daya cikin goma na kudin. Yanayi ne na ban tausayi ga makarantar da kuma al’ummar yankin. Har yanzu ba mu cigaba da karatu ba tun bayan kai harin”.
Ɗaya daga cikin daliban da ke cikin motar lokacin da aka kai harin a ranar Litinin ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru bayan an tashi daga makaranta.
Ya ƙara da cewa masu garkuwar sun umarce su da su fito daga motar daga nan suka zaɓi waɗanda za su dauka suka tafi tare dasu.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci a yi gaggawar ceto mutanen inda ya ba da tabbacin hakan ba za ta ƙara faruwa ba.
A halin yanzu an buƙaci shugabannin tsaro da su gurfana a gaban majalisar dattawa ta kasa a mako mai zuwa domin tattaunawa game da karuwar rashin tsaro da ake fuskanta a kasar.
Yin garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa na kara tsananta a Najeriya cikin shekarun baya-bayan nan inda yan bindiga ke kai farmaki ga mutane masu tafiya a mota da ɗalibai har ma da mazauna ƙarkara da wasu wuraren a biranen da ke sassan ƙasar.