Jami’ai a Burkina Faso sun ce, wasu mayaƙa da ake zargi masu da’awar jihadi ne sun kashe aƙalla mutum 27 a hare-haren da suka kai a ƙauyukan da ke yankin arewacin ƙasar a ƙarshen mako.
Sun ce mutum 15 wasu daga cikinsu yara ƙanana ne aka kashe a harin ranar Lahadi a lardin Kossi.
Mazauna yankin sun ce kusan mutum ashirin aka kashe.
A wani harin kuma, mutum sha biyu aka kashe a lardin Yatenga a ranar Asabar.
Burkna Faso, ɗaya daga cikin ƙasashe matalauta a duniya, na fama da hare-haren ƴan bindiga da suka tsallako daga makwafciyarta Mali a 2015.