fidelitybank

Masu cin naman mutum da siyarwa a Zamfara sun shiga hannun hukuma

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama mutum hudu da zargin sayar da naman sassan jikin dan Adam tare da ci wanda wani abu da ba a saba gani ba a jihar.

A taron manema labarai da ya gudanar a Gusau babban birnin jihar ta Zamfara ranar Alhamis, Kwamishinan ‘yan sanda Ayuba Elkana ya ce, an damke wadanda ake zargin ne bayan da jami’an tsaro suka tsinci gawa a wani kango, ba tare da wasu sassan jikinta ba.

Gano gawar wani bangare ne na bincike da ake yi kan batan wani yaro dan shekara tara.

BBC ta rawaito cewa, tun a makon da ya gabata aka ma mutanen hudu da a ke zargi, da suka hada da wasu magidanta maza biyu da kuma matasa suma maza biyu kamar yadda CP Elkana ya sanar.

Ya kara da cewa yanzu haka ana kan neman wasu mambobin kungiyar da ake zargi da cin naman mutane.

Kazalika kwamishinan ‘yan sandan ya ce kawo yanzu bincike ya nuna cewa sau biyu shugaban kungiyar na tura wa uku daga cikin wadanda aka kama naira 500,000 na cinikin sassan jikin dan adam.

Cin nama da sayar da sassan jikin mutane wani sabon abu ne a Zamfara, duk da jihar ta yi kaurin suna wurin kashe-kashe da garkuwa da mutane don neman kudin fansa daga ‘yan bindiga tsawon shekaru.

Kuma hukumomin Najeriya na shan suka saboda nuna gazawa wurin shawo kan halin da jihar ke ciki.

A wata mai kama da haka yayin zantawa da manema labaran CP Ayuba Elkana ya ce jam’ian tsaro sun kubutar da mutun 17 da aka sato daga jihar Neja aka shiga da su Zamfara.

Ya kara da cewa yayin wani sintiri, ‘yan sanda sun kwato makamai da suka hada da bindigar harba makamin roka, bayan bata kashi da ‘yan bindiga a wani daji da ke yankin.

A makon da ya gabata ne ‘yan fashin daji suka kashe kusan mutun 200, a lokacin da suka kai wasu jerin hare-hare a kauyukan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

yola news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka Æ´an Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation HaÉ—in-Kai sun ce sun kashe Æ´an...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aÆ™alla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naÉ—a shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp