Shugaban kungiyar dattawan kishin kasa ta Najeriya, Dr Bature AbdulAziz, ya caccaki masu kiran a dakatar da rantsar da zababben shugaban kasa, Sanata Bola Tinubu.
AbdulAziz ya bayyana cewa, kiran a dakatar da rantsar da zababben shugaban kasa tamkar kira ne na rashin zaman lafiya.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, Asabar, ya ce wasu mutane na jahannama kan haddasa rashin tabbas a cikin al’umma.
“Me yasa kuke kiran a dakatar da rantsuwa? Abin da kuke nema, shin yana da wani matsayi a doka ko a tarihin Najeriya?” Ya tambaya.
Ya ce doka ta nuna karara cewa zababben shugaban kasa ko Gwamna ko kuma duk wanda zai iya yin rantsuwa a yayin da lamarin ke kai kara kotu.
“Don haka, me ya sa wasu ke kashe kansu da sunan neman hana rantsuwa, wannan ba shi da tushe, suna magana ne bisa jahilci,” inji shi.