fidelitybank

Masu burin zama shugaban kasa kamata ya yi a ce suna gidan Yari – Obasanjo

Date:

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce, wasu masu burin zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ya kamata a ce suna gidan yari idan da hukumomin da ke yaƙi da rashawa a Najeriya suna aikinsu yadda ya dace.

Tsohon shugaban ya faɗi haka ne a wani babban taron ƙara wa juna sani da aka gudanar a Abeokuta jihar Ogun domin bikin cikarsa shekara 85 da haihuwa, kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.

“Na kalli wasu daga cikin mutanen da ke yawo da kuma wadanda mutane ke yawo da su. Idan da EFCC da ICPC za su yi aikinsu yadda ya kamata da kuma goyon bayan ɓangaren shari’a, da yawancinsu suna gidan yari.”

Duk wanda da ba shi da gaskiya a ƙananan abubuwa, ba zai iya gaskiya ba manyan abubuwa,” in ji Obasanjo.

Tsohon shugaban na Najeriya ya kuma ce babu wani ɗan takara a yanzu da yake goyon baya, duk da ya ce wasu daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa sun kai masa ziyara suna neman goyon bayansa.

Obasanjo ya kuma ƙaryata rahotannin da suka lissafa wasu ƴan takara a yankin kudu da yake marawa baya.

“A irin wannan hali da muke ciki, ba zan yi gaggawar faɗin sunaye, ba tare da tuntuɓa ba da kuma tabbatar da ingantattun ka’idoji da matakai ba,” in ji shi.

daily post news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp