Kungiyar masu bukata ta musamman ta kasa, ta yi kira ga gwamnati da ma sauran masu ruwa da tsaki a kan a biya mata wasu muradunsu guda uku.
Kungiyar ta yi kiran ne a wajen wani taron ranar tunawa da masu bukata ta musamman da aka yi a Abuja babban birnin tarayya.
Kungiyar ta shaida wa BBC cewa, abubuwan da ta ke so a biya mata bukatun a kansu sun hadar da shigar da mutanensu cikin tsare-tsaren bangaren bankuna da ma sabbin tsare-tsaren da Babban Bankin Kasar ya kawo a kwanan nan.
Shugaban kungiyar Isiyaku Adamu Gombe, ya ce, ko kadan Babban Bankin Najeriya ba ya la’akari da wasu daga cikinsu musamman marasa gani idan zai bullo da wasu tsare-tsare.
Ya ce, a don haka suke so gwamnatin tarayya ta sa a rinka tunawa da su a dukkan wani abu da za a fito da shi sabo.
Abu na biyu da kungiyar ta bukaci gwamnati ta yi mata shi ne batun dokar hakkin mallakar da ke gaban majalisa a yanzu, suna bukatar shugaban kasa ya sanya hannu a kai saboda akwai abin da ya shafi mutane masu bukata ta musamman a ciki.
Sai abu na uku da kungiyar ta ce tana so a yi mata shi ne, ‘yan takara da jam’iyyun Najeriya su rinka sanya manufofi na masu bukata ta musamman a dukkanin manufofin da suke son yi wa kasa ko jiha.
Isiyaku Adamu Gombe, ya ce suna da bukatu da suke so a cika musu a don haka suna so su ji manufofin ‘yan takara don su san wadanda za su zaba.
Kidididga ta nuna cewa mutane masu bukata ta mussamman a Najeriya sun kai kashi 15 cikin dari na al’ummar kasar, wato kimanin mutane sama da milyan 30 ke nan.