Masu amfani da shafin Tuwita sun zabi Elon Musk ya sa sauka daga shugabancin kamfanin, bayan da ya wallafa wani sakon jin ra’ayin masu amfani da shafin a kan makomarsa.
Kashi 57 cikin 100 na masu amfani da shafin sun zabi cewa shugaban kamfanin ya sauka.
Mr Musk, wanda ya sayi kamfanin a kan dala biliyan 44, ya ce zai amince da abin da sakamakon ya bayyana.
Mr Musk, wanda shi ne mai kamfanin Tesla da kuma Space X, na fuskantar suka tun bayan da karbe ragamar tafiyar da kamfanin.
Har kawo yanzu bai ce uffan ba tun bayan kammala zaben, to amma ko da ya sauka daga kan shugabancin kamfanin, zai ci gaba da kasancewa mai kamfanin.
Fiye da mutane miliyan 17 da miliyan 500 ne suka kaÉ—a Æ™uri’ar a ranar Litinin, inda kaso 42.5 cikin 100 ne kadai suka zabi rashin amincewa da murabus din nasa.