Ƴan majalisa a Indonesia, sun amince da sabuwar dokar da ta haramta jima’i kafin aure, inda yanzu hakan ya zamo babban laifi, wanda aka samu da lifin ka iya zaman kason sama da shekara guda.
Dokar dai ta shafi ƴan ƙasa da baki na ƙasashen waje kamar ƴan yawon buɗe ido.
A ƙarƙashin sabuwar dokar laifi ne jima’i kafin aure, wanda za a iya yankewa mutum hukuncin sama da shekara, kuma an haramta daduro kafin aure.
Sannan an bai wa iyaye ko ma’aurata damar kai rahoto idan ɗansu ya aikata laifin, ko mata ko miji domin ayi musu hukunci.