Likitan tiyatar zuciya kuma mai fafutukar kawo sauyi Masoud Pezeshkian ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a Iran.
Dan majalisar wanda ya yi alkawarin tuntubar kasashen yammacin duniya domin yin gyare-gyare domin mayar da Iran gaba don samun ci gaba ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar bayan doke abokin hamayyarsa Saeed Jalili mai fafutuka.
Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta ce “Ta hanyar samun rinjayen kuri’un da aka kada ranar Juma’a, Pezeshkian ya zama shugaban kasar Iran.”
Pezeshkian ya samu kashi 53.7 na kuri’un da aka kada, wato miliyan 16.3; yayin da Jalili ya samu kashi 44.3 ko miliyan 13.5.
Pezeshkian ya ce a cikin jawabinsa na farko a bainar jama’a bayan sanar da sakamakon zaben cewa ba shi ne wanda ya yi nasara ba.
“Dukkanmu mutanen kasar nan ne; za mu yi amfani da kowa don ci gaban kasa,” inji shi a gidan talabijin na kasar.
Ba da dadewa ba bayan bayyana sakamakon zaben, Jalili ya amince da shan kaye, inda ya nemi ‘yan Iran da su mutunta zababben shugaban kasar.
“Ba wai kawai ya kamata a mutunta shi ba, amma yanzu dole ne mu yi amfani da dukkan karfinmu kuma mu taimaka masa ya ci gaba,” in ji shi a gidan talabijin.
Shiga zaben ya kai kashi 49.8 cikin 100 a fafatawa tsakanin Pezeshkian da Jalili.
Zaben zagaye na biyu na ranar Juma’a ya biyo bayan jefa kuri’a ne a ranar 28 ga watan Yuni na zaben magajin Ebrahim Raisi wanda ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a watan Mayu.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun yi imanin cewa nasarar da Pezeshkian ya samu na iya ganin ci gaban manufofin ketare na zahiri, da sassauta tashin hankali kan tattaunawar da aka yi da manyan kasashen duniya don farfado da yarjejeniyar nukiliyar 2015 da kuma kyautata fatan samun ‘yancin walwala a Iran.