Allah ya yi wa Aminu S Bono, mashiryin fina-finai a masana’antar Kannywood Rasuwa.
Ya rasu a yammacin yau Litinin, bayan ya yanke jiki ya faɗi jim kaɗan bayan dawowarsa daga aiki.
Makusanta sun tabbatarwa da rasuwar jarumin masana’antar ta Kannywood.