Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje ya dage cewa masarautun da gwamnatinsa ta kirkiro mahadi ka ture ne.
Ganduje ya ce zai ci gaba da addu’a kada a lalata masarautun bayan ya bar mulki.
Bayanin gwamnan ya zo ne kwanaki bayan jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, dan takarar shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso, ya ce gwamnatin Abba Yusuf mai jiran gado za ta sake duba salon mulkin masarautar Kano.
Ganduje ya raba masarautun Kano gida biyar bayan da ya tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na lokacin.
Gwamnan ya ce, sabbin masarautun hudu alama ce ta hadin kai, ci gaba, da walwala.
Sai dai a jawabin da ya yi yayin bikin ranar ma’aikata a Kano, Ganduje ya ce an kirkiro masarautun ne domin al’umma.
A cewar Ganduje: “Duk wanda ya ziyarci hedikwatar wadannan sabbin masarautun zai yarda cewa mun kawo ci gaba a wadannan wuraren.
“Ko da ba a gwamnati muke ba, muna addu’a kuma za mu ci gaba da addu’ar Allah ya kare wadannan masarautun daga dukkan sharri. Na gode muku duka.”