Masarautar Rano a Kano ta haramta cire yarinya daga makaranta domin aurar da ita kafin ta kammala karatun firamare.
Sanarwar da sakataren yada labaran masarautar, Nasiru Habu Faragai, ya aike da manema labarai a Jumu’ar nan,
Ya ce Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umaru, ya bayyana hakan ranar Alhamis, yayin bikin ƙaddamar da ɗaukar sababbin daliban aji ɗaya na shekara ta 2025/2026, wanda Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta Jiha (SUBEB), tare da haɗin gwiwar UBEC da UNICEF, suka shirya a garin Lausu da ke masarautar Ranon.
Sanarwar ta ce Sarkin ya umarci dagatai, masu unguwanni, sarakunan Fulani da limamai da su tabbatar da bin wannan doka, tare da gargadin cewa duk wanda ya saba mata za a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.
Haka kuma, Sarkin ya gargadi iyaye da malamai da kan su guji hada baki wajen cire yarinya daga makaranta don yi mata aure, yana mai cewa wannan mataki ne da zai hana ci gaban rayuwar yara.
Sarkin ya bukaci iyaye da shugabannin al’umma su ba da haɗin kai da goyon bayan da ake buƙata ga gwamnati a ƙoƙarinta na inganta ilimi a jihar Kano.