Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya yi kira ga masu rike da tutar jam’iyyar APC da su rungumi wadanda suka sha kaye a zaben fidda gwani na shirin tunkarar zaben 2023.
Ya yi wannan roko ne a lokacin da ya karbi bakuncin taron masu ruwa da tsaki da kwamitin tuntubar jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma a Katsina.
A cewar gwamnan, hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar APC ya kasance hanyar samun nasara a zabe.
Masari ya yabawa shugabancin jam’iyyar a jihar bisa kafa kwamitocin sasantawa domin jinyar raunata da aka samu a zaben fidda gwanin da ta yi.
Gwamnan ya bukaci shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar da su jajirce wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa.
Alhaji Salihu Muhammed, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa a yankin arewa maso yamma, wanda ya halarci taron, ya ce taron na da nufin yin sulhu a matsayin hanyar samun nasara a zaben 2023 mai zuwa.
Ya ce, tuni kwamitin tuntubar ya gabatar da rahoton share fage daga jihohi biyar a baya sannan ya ziyarci Masari a wani taron da aka yi a Abuja tun farko.