Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi kira ga ‘yan siyasa a Najeriya da su guji duk wata siyasa da za ta cutar da rayuwar kasar nan.
A cewarsa, irin wannan salon siyasar ba zai dore da ci gaban kasa da tafiyar siyasar kasar ba.
Masari ya yi wannan kiran ne a lokacin da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnatin jihar, domin sanar da Gwamnan Katsina a hukumance aniyarsa ta tsayawa takarar Shugabancin Tarayyar Najeriya.
Wike ya je jihar Katsina ne a ranar Talata, domin tuntubar wakilan jam’iyyar PDP, gabanin babban taron jam’iyyar na kasa a karshen wannan watan.
Masari ya ce: “ Kirana ga ‘yan siyasa shi ne su rika taka wannan siyasa ta yadda al’umma da tsarin siyasarta za su ci gaba da wanzuwa.