fidelitybank

Masarautar Saudiyya ta ɗage dokar hana jiragen sama daga Najeriya da wasu ƙasashe 16

Date:

Masarautar Saudiyya ta ɗage dokar hana zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya da wasu kasashe 16.

Sauran kasashe sun hada da Afirka ta Kudu, Namibiya, Botswana, Zimbabwe, Lesotho, Eswatini, Mozambique, Malawi, Mauritius, Zambia, Madagascar, Angola, Seychelles, Jamhuriyyar Comoros, Habasha da Afghanistan.
Sabon tashar Lafia zai zama cibiyar watsa labarai ta Najeriya -NDPHC

Hakazalika, mahukuntan Saudiyya sun kawo karshen bayar da tazara ga jama’a a cikin masallatai biyu masu tsarki a cikin masarautar, amma sun dage da rufe hanci da baki, yayin da suke isa wurin ibada.

Hakan dai na zuwa ne a bisa wata umarni da ma’aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta fitar, kuma mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad ya tabbatar a shafin Twitter.

Saudi Gazette ta ba da rahoton cewa, matafiya ba za su ƙara yin keɓewar COVID-19 na tilas ba idan sun isa Masarautar.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa (GACA) a kasar Saudiyya ta tabbatar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya a wata takardar da ta aikewa dukkan kamfanonin jiragen sama da ke aiki a Saudiyya a ranar 8 ga watan Disamba, 2021.

A watan Janairun 2022, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bukaci Saudiyya da ta dage takunkumin hana zirga-zirgar da ta sanya wa matafiya ‘yan Najeriya, biyo bayan bullar kwayar cutar COVID-19 a Afirka ta Kudu da aka gano a tsakanin wasu matafiya da aka ce sun ziyarci Najeriya.

Ambasada Zubairu Dada, karamin ministan harkokin wajen kasar ne ya yi wannan roko a cikin wata sanarwa da kakakinsa Ibrahim Aliyu ya fitar, yayin da ya yaba da kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu tsawon shekaru.

nan news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp